Babban jami'i mai kula da aikin ba da shawara kan harkar siyasa na kasar Sin Wang Yang, ya ziyarci yankin raya masana'antu na kasar Uganda, inda ya yi kira ga kamfanonin kasar Sin, da su kara azama a aikin bunkasa masana'antun nahiyar Afirka, da inganta matakan samar da hajoji a cikin nahiyar, tare da kara fadada hada hadar cinikayya a Afirka.
Wang, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin koli na majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ko CPPCC a takaice, ya ziyarci yankin na Liaoshen dake garin Kapeeka, a gundumar Nakaseke a ranar Alhamis, a wani bangare na ziyarar yini hudu da yake gudanarwa a kasar ta Uganda dake gabashin Afirka. (Saminu Alhassan)