Rahotanni daga hukumar gidan waya ta kasar Sin na nuna cewa, tun lokacin da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga waje, ya zuwa yanzu, hukumar ta samu riba mai tsoka yayin da al'ummomin kasar ke kara cin gajiyar ayyukan hukumar, biyo bayan kwaskwarimar da aka yi a tsarin aikewa da kayayyaki da wasiku, a halin yanzu, hukumar ta kara inganta ayyukanta na aikewa da wasiku da kayayyaki cikin sauki a nan kasar Sin.
Bayanai na cewa, ya zuwa karshen shekarar 2017, ayyukan aikewa da kayayyaki da wasiku ya karade kaso 87 cikin 100 na garuruwa da kauyuka a duk fadin kasar Sin, lamarin da ya biyan bukatun mazauna kauyuka kimanin miliyan dari 6 a wannan fanni. Sa'an nan, a shekarar 2018, ana ci gaba da kara kyautata wannan aiki, ya zuwa yanzu, ayyukan hukumar a garuruwa da kauyuka na fadin kasar Sin ya kai sama da 90%. (Maryam)