Yarjejeniyar dai za ta baiwa sassan biyu damar yin musayar kudade da suka kai Yuan biliyan 15, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2.35, kan kudin Najeriya Naira biliyan 720 tsakanin shekaru 3 masu zuwa.
Wata sanarwar da babban bankin na Sin ya fitar kan shafin sa na yanar gizo, ta ce daukar wannan mataki na da nufin karfafa dangantakar cinikayya, da zuba jari, da daidaita yanayin hada hadar kudade tsakanin sassan biyu.