Gabanin taron gidauniyar na bana da zai gudana a Tianjin na kasar Sin, Klaus Schwab, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, cikin sama da shekaru 40 da suka gabata, an yi ta suka tare da hasashen cewa ci gaban tattalin arzikin kasar Sin zai kawo karshe, sai dai kuma hakan bai tabbata ba.
Alkaluman GDP na kasar Sin ya karu da kaso 6.8 cikin rabin farko na bana, wanda ya zarce hasashen da gwamnati ta yi na kusan kaso 6.5. ci gaban tattalin arzikin ya tsaya ne tsakanin kaso 6.7 da 6.9 cikin rubu'i 12 a jere, al'amarin dake nuna juriyar tattalin arzikin kasar. (Fa'iza Mustapha)