Yau Alhamis kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya sanar da cewa, bisa gayyatar da shugaban masarautar hadaddiyar Daular Larabawa, da shugaban janhuriyar kasar Senegal, da shugaban janhuriyar kasar Ruwanda, da shugaban jamhuriyar kasar Afirka ta Kudu suka yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gudanar da ziyarar aiki a wadannan kasashe hudu, tsakanin ranekun 19 zuwa 24 ga wannan wata na Yuli.
Kana bisa gayyatar da shugaban Afirka ta Kudu ya yi masa, shugaba Xi zai halarci taron ganawa tsakanin kasashen mambobin BRICS karo na 10, wanda za a shirya a Johannesburg, tsakanin ranekun 25 zuwa 27 ga watan Yulin da muke ciki.
Bayan kammala dukannin ayyukan, shugaba Xi zai yada zango a kasar ta Mauritius, inda zai gudanar da ziyarar sada zumunta.(Jamila)