Shugaban hukumar zartaswar kungiyar hadin kan Afirka ta AU Moussa Faki Mahamat, ya jinjinawa ci gaban da aka samu, game da dangantakar kasashen Habasha da Eritrea.
Wata sanarwa da AUn ta fitar a Alhamis din nan ce ta tabbatar da hakan.
Kasashen biyu dake yankin gabashin Afirka sun fafata yaki a kan iyakar su, tsakanin shekarun 1998 zuwa 2000, kafin su kai ga sanya hannu kan yarjejeniyar birnin Algiers a cikin watan Disambar shekara ta 2000.
A kuma ranar 5 ga watan Yuni ne kwamitin zartaswa na jami'iyyar EPRDF dake mulki a Habasha, ya ayyana burin kasar na tabbatar da an aiwatar da yarjejeniyar Algiers ta watan Disambar shekarar 2000.
Moussa Faki Mahamat, ya ce sanarwar da mahukuntan Habasha suka fitar a ranar 5 ga watan Yuni, ta jaddada burin su, na aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma yadda ya kamata, da kuma kudurin shugaba Isaias Afwerki na Eritrea, wanda ya bayyana a ranar 20 ga watan Yuni, na tura wata tawagar wakilai zuwa birnin Addis Ababa, a wani mataki na tattaunawa da tsagin Habasha, lamarin da kuma shi ma firaministan kasar ta Habasha Abiy Ahmed ya yi maraba da shi.(Saminu)