A yayin bikin, dan sarki Andrew ya ce, bikin da aka yi a birnin London ya bada ma'ana kwarai da gaske, domin littafin zai yi bayani ga karin mutane kan kasar Sin, da kuma irin makoma da take nema. Ya kuma nuna fatan cewa, za a sami karin mutane da su kai ziyara a kasar Sin da kansu.
A nasa bangare kuma, Jiang Jianguo ya ce, littafin mai taken "Ra'ayoyin Xi Jinping Kan Gudanarwar Harkokin Mulkin Kasa" ya nuna ci gaban tsarin gurguzu a kasar Sin a yayin da Xi Jinping yake jagorancin kasar. Haka kuma, an yi imanin cewa, ta hanyar karanta wannan littafi, mutanen kasa da kasa za su iya zurfafa fahimtarsu kan Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, wadda take dukufa wajen tallafawa al'umma, da neman farfadowar kasa da kuma dunkulewar kasa da kasa baki daya.
An fassara littafin zuwa harsuna guda 9, wanda aka fara sayar da su a hukumance bayan bikin da aka yi a birnin London. Kuma wadannan harsuna guda 9 sun hada da bakaken gargajiya na Sinanci, Turanci, Faransanci, Spaniyanci, Jamusanci, Rashanci, Japananci, Larabci da kuma harshen Portugal. (Maryam)