Xi ya ce, kawar da talauci na da muhimmiyar ma'ana, ga gina kasar Sin mai matsakaicin ci gaba a dukkanin fannoni. Don haka ya kamata gwamnatoci a matakai daban-daban, su maida aikin kawar da talauci a matsayin babban aikin siyasa, da nuna himma da kwazo wajen gudanar da aikin. Bugu da kari, kamata ya yi gwamnatoci da kasuwanni, su hada gwiwa don tallafawa matalauta ta hanyoyi daban-daban.
A nasa bangaren ma, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya nuna cewa, ya zama dole sassa daban-daban na kasar su yi kokarin taimakawa mutane masu fama da talauci, don kyautata zaman rayuwarsu, ta yadda za'a cimma burin kawar da talauci yadda ya kamata.(Murtala Zhang)