Asusun IMF ya yaba wa kasar Sin kan nasarorin da ta samu ta fannin yin kwaskwarima
A jiya Talata ne asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin na kara samun ci gaba mai dorewa, kuma kasar ta samu ci gaba a gyare-gyaren da take yi a fannoni da dama, ana kuma hasashen bunkasuwar tattalin arzikin kasar zai kai kimanin kashi 6.7% a wannan shekara.
Asusun ya bayyana haka ne bayan da ya kammala yin shawarwari dangane da tattalin arziki da manufofi tare da kasar ta Sin.
Bayan shawarwarin, asusun na IMF ya bayyana cewa, sakamakon wasu manufofi da karuwar bukatun waje da kuma ci gaban gyare-gyaren da ake gudanarwa a cikin gida, ana hasashen tattalin arzikin kasar zai bunkasa sosai. (Lubabatu Lei)