A yayin bikin da aka yi mai taken "Taya murnar cika shekaru 25 wajen aiwatar da aikin kiyaye bambance-bambancen halittu masu rai", mataimakin ministan kula da harkokin muhalli na kasar Sin Huang Runqiu ya bayyana cewa, adadin dabbobin dake bakin karewa wadanda suke zama cikin gandun daji, da suka hada da panda, damisar yankunan arewa masu gabas, da kuma gwankin yankin Tibet, da dai sauransu, ta yadda za su karu cikin yanayin zaman karko.
Haka kuma, kasar Sin za ta gina zirin muhallin halittu da tsarin intanet na kare bambance-bambancen halittu masu rai, domin karfafa ayyukan sa ido kan ayyukan.
Babbar sakatariyar zartaswa ta yarjejeniyar kare bambance-bambancen halittu masu rai Cristiana Pasca Palmer ta bayyana cewa, tun lokacin da kasar Sin ta kulla yarjejeniyar, ta ci gaba da mai da hankali kwarai da gaske kan aikin kiyaye bambance-bambancen halittu masu rai, inda ta kuma mai da aikin a matsayin muhimmin matakin inganta gina tsarin kiyaye muhalli. (Maryam)