Kafin haka, babban darektan hukumar kare muhalli ta MDD, Erik Solheim, ya furta cewa, yadda kasar Sin take kokarin hana shigo da shara cikin kasar, wani sako ne ga wasu kasashe masu sukuni, wanda ya bayyana cewa kamata ya yi a inganta tsarin bola-jari, da rage samar da kayayyakin da al'umma ba ta bukatarsu.
A nasa bangaren, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya ce gwamnatin kasar Sin ta dauki matakin hana shigo da shara cikin kasar sabo da muhimmiyar manufarta ta kare muhalli, da tabbatar da lafiyar al'ummar kasar.(Bello Wang)