Lu ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Litinin. Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye tare da martaba yarjejeniyar.
Rahotanni na cewa, a ranar 25 ga wannan wata ne kasashen Iran, Sin, Rasha, Faransa, Jamus da kuma Burtaniya za su shirya wani taron hadadden kwamiti game da yarjejeniyar nukiliyar Iran a dukkan fannoni ne. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Seyed Abbas Araqchi ya ce, a yayin taron za a tattauna tasirin da janyewar Amurka ta yi daga yarjejeniyar, da kuma yadda bangarori daban daban da batun ya shafa za su ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar. (Bilkisu)