Geng Shuang ya ce, a wannan karo, Mr. Zarif zai ziyarci kasashen Sin, da Rasha da wasu kasashen Turai, domin yin musayar ra'ayoyi kan batun makamashin nukiliyar kasar Iran. Kuma kasar Sin na daya daga cikin wadanda suka kulla yarjejeniyar batun makamashin nukiliyar kasar Iran, shi ya sa tana mai da hankali sosai kan wannan batu.
A sa'i daya kuma, Sin tana fatan gudanar da shawarwari da dukkan kasashen da batun nukiliyar kasar Iran din ya shafa, ciki har da ita kanta kasar ta Iran. (Maryam)