Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang, ya ce kasar sa ta yi takaicin janyewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran wadda aka daddale a shekarar 2015.
Geng Shuang wanda ya bayyana hakan a Larabar nan, ya ce ya kamata dukkanin masu ruwa da tsaki a yarjejeniyar, su aiwatar da ita kamar yadda ya dace, su kuma martaba kima da kuma darajar ta.
Geng ya kara da cewa, aiwatar da wannan yarjejeniya na da ma'anar gaske, wajen cimma nasarar da aka sanya gaba, game da kokarin dakile yaduwar makaman nukiliya a duniya, da wanzar da zaman lafiya da daidaito a gabas ta tsakiya. Kana hakan zai zama 'yar manuniya ta muhimmancin da ake baiwa manufar warware sabani tsakanin kasashen duniya ta hanyar siyasa.
Daga nan sai ya bayyana burin kasar Sin, na ganin dukkanin kasashe masu ruwa da tsaki a sha'anin nukiliyar Iran, sun ci gaba da daukar matakai mafiya dacewa a yanzu da ma nan gaba, su kuma nacewa hanyar warware sabani ta hanyar tattaunawa da dabarun diflomasiyya. Da fatan ba da dadewa ba, za a kai ga komawa hanyar aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar.(Saminu Alhassan)