in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya na mai da hankali sosai kan janyewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliya ta Iran
2018-05-09 13:48:02 cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a jiya 8 ga wata cewa, Amurka ta yanke shawarar janye jikinta daga yarjejeniyar nukiliya ta Iran da dawo da takunkumin da ta sakawa Iran. Saboda haka, kasashen duniya na mai da hankali sosai kan lamarin, har ma shugabannin kasashe da kungiyoyi daban-daban, sun sanar matsayin da suka dauka.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta ba da sanarwa a wannan rana cewa, Rasha na bayyana rashin jin dadi matuka saboda matakin da Amurka ta dauka. Rasha na fatan ci gaba da kara tuntubar bangarori masu ruwa da tsaki na yarjejeniyar, tare kuma da kara hadin kai da Iran.

Ban da wannan, shugaban Faransa Emmanuel Macron da firaministar Birtaniya Theresa Mary May da takwaranta ta Jamus Angela Dorothea Merkel, sun ba da haddadiyar sanarwar a wannan rana, wadda ta yi bakin ciki ga matakin da Amurka ta dauka, tana mai cewa, kasashen za su ci gaba da bin yarjejeniyar.

Ita ma ma'aikatar harkokin wajen kasar Sham, ta fitar da sanarwar da ta yi tir da wannan shawarar da Amurka ta yanke.

Shi kuwa firaministan Isra'ila Benjemin Netanyahu, goyon bayan janye jikin da Amurka ta yi ya yi. Cikin wata sanarwa ta telibijin Benjemin Netanyahu, ya ce Isra'ila ba ta amince da wannan yarjejeniya ba tun da farko, a ganinsa, kawar da takunkumi a kan Iran babban kuskure ne, matakin da ya haifar da mumunan tasiri. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China