Bangarorin biyu na ganin cewa, raya huldar tattalin arziki da cinikayya ta hanyar da ta dace, yana da matukar muhimmanci ga kasashensu, kana, za su warware matsalar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu ne ta hanyar yin shawarwari.
Bangarorin biyu sun yi musanyar ra' ayi kan wasu batutuwa, ciki har da yadda Amurka za ta kara fitar da hajoji zuwa kasar Sin, da zuba wa juna jari, da kare ikon mallakar fasaha, da daidaita matsalar harajin da suke sanyawa hajojin juna da sauransu, inda suka cimma matsaya daya kan wasu fannoni.
Har wa yau, bangarorin biyu na ganin cewa, akwai bukatar a kara yin kokari, saboda har yanzu akwai sabanin ra'ayi a tsakaninsu.(Murtala Zhang)