in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi Allah wadai da tashin hankalin da ya biyo bayan wasan kwallon kafa a filin wasa na firka Moses Mabhida
2018-04-25 13:42:02 cri

Mahukuntan kasar Afirka ta kudu da sauran masu ruwa da tsaki a fannin wasanni, sun yi Allah wadai da tashin hankalin da wasu bata gari suka haddasa a filin wasan kwallon kafa na Moses Mabhida dake Afirka ta kudu, lamarin da ta haifar da jikkatar mutane 18.

Wasu 'yan kallo ne dai suka afka cikin filin wasan a karshen mako, bayan da aka doke kungiyar su da ci 2 da nema a gasar cin kofin Nedbank, inda nan take suka haifar da hargitsi wanda ya lahanta wasu 'yan kallo.

Da yake tsokaci game da aukuwar lamarin, ministan wasanni na kasar Tokozile Xasa, ya ce dole ne a bayyana hakikanin abun da ya auku da almurun ranar Asabar, bayan wasan da aka doke kungiyar night Kaizer.

Rahotanni sun bayyana cewa, magoya bayan kungiyar sun kaiwa masu gadin filin wasan hari, sun kuma lalata wasu kayayyakin wasa dake cikin filin, baya ga wadanda aka raunata su 18. Kawo yanzu dai an kama mutane 2 bisa zargin su da hannu a aukuwar lamarin.

Ita ma hukumar wasanni ta Afirka ta kudu Sascoc, ta yi Allah wadai da aukuwar tashin hankalin. A cewar shugabanta Gideon Sam, ba za a taba amincewa da wannan halayya ba.

Gideon Sam ya ce, hukumar kwallon kafar kasar PSL, da shugabannin filin wasan, dole ne su yi bayani game da abun da ya faru. Ya ce tashin hankali ba zai taba warware wata matsala ba. Kaza lika ya kara da cewa, ba za su taba kyalewa magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa suna haifar da tashin hankali ba, musamman ma duba da yadda wasan kwallon kafa ke hade kan al'umma.

Ya ce yana fatan dukkanin masu ruwa da tsaki za su hada kai da Afirka ta kudu wajen tabbatar da hukunta wadanda suka aikata wannan laifi.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China