in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco ta bayyana karfin gwiwar ta game da daukar nauyin gasar cin kofin duniya ta 2026
2018-04-04 16:56:21 cri

Mahukuntan kasar Morocco, sun bayyana kwarin gwiwar da suke da shi, game da ikon su na cimma nasarar daukar nauyin gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa na shekarar 2026, idan har hukumar FIFA ta ba ta wannan dama a zaben da za a yi ranar 13 ga watan Yunin wannan shekara da muke ciki.

Da yake karin haske game da hakan, jagoran ofishin da aka dorawa alhakin nemawa kasar ta Morocco wannan dama Hicham El Amrani, ya ce Morocco ta yi sa'ar kasancewa a wuri mafi dacewa, a yankin da take sama da sauran abokan takarar ta wato kasashen Amurka da Canada da kuma Mexico.

Jami'in ya ce gasar ta cin kofin duniya za ta hada kasashen turai 16, da na Afirka 9, dake kan lissafin agogo iri daya. Ya ce duk da yake Morocco ba ta da kayayyakin gine gine da za a bukata wadanda suka kai na sauran kasashen dake nahiyar Arewacin Amurka 3, dake neman karbar bakuncin wannan gasa, a hannu guda El Amrani na ganin mahukuntan ta, suna marawa aniyar ta baya matuka da gaske. Hakan dai na nufin kasar za ta iya samar da filayen wasa da hanyoyin sufuri, da sauran abubuwan da ake bukata nan da shekaru 8 kafin zuwan lokacin gasar.

El Amrani ya ce "Idan da za a gudanar da gasar a yau ne, to da sai mu ce ba za mu iya karbar bakuncin ta ba". "Amma muna da tsari cikakke na samar da filayen wasa 14, domin gasar ta cin kofin duniya a biranen kasar mu 12, ciki hadda babban fili mai cin mutane 93,000 dake birnin Casablanca wanda za a yiwa kwaskwarima, a kuma gudanar da wasan karshe a cikin sa".

El Amrani, wanda ya taba rike mukamin sakataren hukumar wasannin kwallon kafa ta nahiyar Afirka ko CAF a takaice tsakanin shekarun 2011 zuwa 2017, ya kara da jaddada imanin sa, game da gudanar gasar cin kofin kwallon kafar na duniya a kasar ta Morocco cikin kyakkyawan yanayi na tsaro.

Za dai a tabbatar da kasar da za ta karbi bakuncin gasar ta cin kofin duniya da hukumar FIFA ke shiryawa, wadda kuma za ta gudana a shekarar 2026, a karon farko da kungiyoyin kasashe 48 za su fafata, inda mambobin hukumar FIFA 211 za su jefa kuri'u dai-dai ko wannen su, banda wakilan kasashe 4 da ke neman karbar bakuncin gasar, maimakon yadda ake yi a baya, inda manyan jami'an hukumar kadai ke da ikon jefa kuri'u.

Morocco za ta bukaci kuri'u 104, yayin zaben da za a gudanar kwana guda gabanin bude gasar cin kofin duniya ta kasar Rasha, wadda ke tafe cikin wannan shekara kafin ta samu nasarar da take nema.

Idan aka yi duba da wakilai 53, wadanda za su kada kuri'un su daga hukumar CAF ta nahiyar Afirka, da kuma mambobin hukumar kwallon kafar nahiyar Asiya ta AFC mai wakilai 47, wadda ita ma ake sa ran za ta goyi bayan kasar ta Morocco, akwai yiwuwar Moroccon za ta samu kusan rabin jimillar kuri'un da za a kada ke nan.

Rahotanni na cewa akwai wasu karin kasashe masu magana da yarin Faransanci kamar Faransa da Belgium, da ma wasu kasashen dake yankin tekun Meditareniya, da tuni suka nuna alamun za su marawa Moroccon baya.

Bisa hakan Mr. El Amrani na ganin ko shakka babu, kasar sa na da kwarin gwiwar cimma nasarar da ta sanya gaba. Ya ce wannan ne karo na 5 da kasar Morocco ke neman a bata damar karbar bakuncin gasar ta cin kofin duniya, kuma yanzu ta shirya tsaf domin cimma wannan buri.

Har ila yau jami'in ya ce sun shirya yin aiki tare da sauran al'ummar duniya a wannan gagarumin aiki. Kaza lika sun amince da ikon wasan kwallon kafa na sauya rayuwar al'umma zuwa kyakkyawan yanayi da ake fata.

Ana sa rana gasar ta shekarar 2026, za ta baiwa tawagar kasar Sin damar shiga a dama da ita, tun bayan damar da ta samu ta farko a shekarar 2002. Mr. El Amrani ya ce Morocco na maraba hannu biyu biyu da kasar Sin zuwa gasar da kasar sa ke fatan samun damar karbar bakunci.

Ya ce "Ina fatan za su samu gurbin buga gasar ta 2026. Amma ko da ma ba su samu damar hakan ba, muna gayyatar su da su zo Morocco, kamar yadda 'yan kasar mu da yawa ke zuwa Sin domin ganin yadda wannan babbar kasa take. Muna matukar farin ciki da zuwan ku" A kalaman El Amrani.

Tuni dai El Amrani, wanda ya taba rike mukamin manajan sashen cinikayya na hukumar AFC tsawon shekaru 8, ya zanta da mataimakin hukumar ta AFC Zhang Jian, game da neman amincewar kasar Sin bisa bukatar Morocco.

Ya ce bukatar Morocco za ta baiwa Sin dama ta gudanar da cinikayya, kasancewar tuni kasar ta zuba dumbin jari a sassan nahiyar Afirka daban daban cikin shekaru 20 da suka gabata.

Ya ce "A gani na, ba wai aiki ba ne neman wannan dama, a'a wata dama ce, da martabawa, domin za aka ji matsin lamba daga dukkanin al'ummun kasar ka, da ma nahiyar ka, bisa goyon bayan su na ganin an kai ga cimma bukata. Amma ni hakan na kara san ya ni farin ciki. Ina kuma fatan za mu kai ga nasara". (Saminu Alhassan)

Algeria ta lamincewa Morocco ta karbi bakuncin gasar kwallon kafar duniya a 2026

Ministan wasannin kasar Algeriya, El Hadi Ould Ali, ya tabbatar da cewa kasarsa ta amincewa makwabciyarta Morocco data shiga takarar neman karbar bakuncin gasar wasan kwallon kafa ta hukumar FIFA ta duniya da za'a gudanar a shekarar 2026.

Ould Ali ya fadawa 'yan jaridu cewa, goyon bayan da kasarsa ta nunawa Morocco ya biyo bayan matsayar da shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika ya dauka ne, kuma suna alfahari da cimma wannan matsaya, injishi.

A 'yan kwanakin da suka gabata, tsohon dan wasan kwallon kafan kungiyar wasan iconic ta kasar Algeriya Lakhder Belloumi, ya bada sanarwa cewa zai kasance a matsayin jakadan kasar Moroccon a gasar kofin duniyar ta 2026.

Belloumi ya nuna tafiyar hawainiya wajen amincewa da karbar tayin da Moroccon tayi masa ne, a sakamakon tsamin dangantaka tsakanin kasar Algerian da Morocco, to sai dai tuni gwamnatin Algerian ta yanke kudurin bashi wannan damar.

Kasar Morocco ta riga ta zabi wasu da dama daga cikin fitattun yan wasan Afrika, da suka hada da Samuel Eto'o, Didier Drogba, da El Hadji Diouf domin su kasance jakadunta a takarar neman karbar bakuncin gasar.

Wasu kafafen yada labaran cikin gida sun rawaito cewa, kasar Morocco ta tuntubi zakaran kungiyar wasan Liverpool dan asalin kasar Masar, Mohamed Salah, da dan kasar Potugal na kungiyar wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo, domin su shiga cikin jerin jakadunta domin ta samu karin damammakin yin galaba a neman takarar karbar bakuncin gasar kofin duniya ta 2026.(Ahmad Fagam)

Morocco ta nuna damuwa wajen tabbatar da adalci a takarar neman bakuncin gasar kwallon kafan duniya

Kasar Morocco ta nuna damuwarta na ganin an tabbatar da adalci da aiwatar da al'amurra a bayyane game da batun takarar neman karbar bakuncin gasar wasan kwallon kafan FIFA ta duniya a shekarar 2026.

A wasikar data gabatarwa shugaban hukumar FIFA, kungiyar wasan kwallon kafan kasar Morocco (FRMF), ta bayyana cewa, ba zata laminci hukumar ta FIFA ta nuna wasu banbance banbance ba a matakan karshe na takarar neman izinin karbar bakuncin gasar wasannin kwallon kafan ta duniya.

Morocco ta bayyana damuwarta ne bayan da hukumar ta FIFA ta fitar da cikakkun bayanai game da ka'idojin takarar neman karbar bakuncin gasar wasannin kwallon kafan ta duniya a shekarar 2026 a cikin wannan mako.

A bisa tsarin ka'idojin, hukumar FIFA ba zata amince da bukatar neman takarar ga duk kasar data gaza samun maki 2 daga cikin maki 5 ba, ko kuma kasar da ta gaza cimman ka'idojin da ake bukata. Ko sharruda, kwanaki uku gabanin jefa kuri'ar da za'a gudanar na takarar a ranar 13 ga watan Yuni a birnin Moscow.

Sai dai jami'an gudanarwar neman takarar na kasar Moroccon sun bayyana cewa, sharrudan da hukumar ta wallafa a cikin bayanan ka'idojin data fitar ya ci karo da bayanan hukumar na asali wanda hukumar ta FIFA ta fitar a watan Oktoban bara.

Jami'an sun yi korafin cewa, an samu kare karen wasu sabbin ka'idoji, sabanin na asali. Kuma wadan nan sabbin ka'idoji ba'a taba nunawa kungiyar wasan ta FRMF ba a lokacin shirye shiryen neman takarar tun da fari.

Morocco ta bukaci shugaban na FIFA da ya mutunta dokoki kuma ya yi watsi da tsauraran ka'idoji domin yin adalci a tsarin neman takarar.

Shugaban neman takarar bakuncin gasar na kasar Morocco Moulay Hafid Elalamy ya bayyana cewa, abune mai matukar wahalar gaske a kai ga cimma nasara idan aka samu alkalin wasa ko mai yin alkalanci marar adalci.

Wannan shine karo na 5 da Morocco ke shiga takarar neman karbar bakuncin gasar kwallon kafa ta duniya, bayan wanda ta nema a shekarun 1994, 1998, 2006 da kuma 2010.

Morocco tana takarar neman karbar bakuncin ne tare da kasashen Amurka, Mexico da Canada.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China