Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Sudan ta kudu (UNMISS), ta kaddamar da shirin gangamin kiyaye haddura a kan titunan mota, inda ya raba daruruwan ababen ba da kariya ga masu amfani da baburan achaba da nufin kare afkuwar haddura.
Shugaban tawagar UNMISS David Shearer, ya fada wa 'yan jaridu cewa, baburan achaba su ne manyan hanyoyin zirga zirgar yau da kullum a Juba da sauran garuruwan dake kewaye a kasar ta Sudan ta kudu, kuma suna da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasar.
Shearer ya lura cewa, mafi yawa daga cikin iyalai sun dogara ne kan wannan sana'ar wajen samun abin biyan bukatun rayuwarsu, a daidai lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki a kasar.
Ana danganta mafi yawan hadduran da ake samu a Juba da tukin ganganci wanda masu baburan achabar ke yi, kana da yawa daga cikin masu aikata fashi da makami suna amfani da babura ne wajen aikata laifukan.(Ahmad Fagam)