Sakataren MDD mai lura da ayyukan wanzar da zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix, ya shaidawa zaman kwamitin tsaron MDD a jiya Laraba cewa, halin da ake ciki a Sudan ta Kudu abun damuwa ne.
Mr. Lacroix ya ce, duk da yarjejeniyar da aka cimma ta dakatar da bude wuta a ranar 21 ga watan Disamba, aka kuma fara aiwatarwa 'yan kwanaki bayan haka, har yanzu babu wani tabbas game da yanayin tsaro a kasar, yayin da ake ta samun karuwar keta hurumin yarjejeniyar.
Ya ce, sassan da ba sa ga maciji da juna na ci gaba da yada farfagandar rura wutar rikici, wanda hakan ke nuni ga rashin kyakkyawar niyya ta martaba yarjejeniyar, matakin dake dada gurgunta kokarin da kasashen yankin, da ma sauran kasashen duniya ke yi na ganin an cimma nasarar wanzar da zaman lafiya a kasar.
Har ila yau Mr. Jean-Pierre Lacroix ya nuna damuwa game da yawaitar keta hakkokin bil Adama, da tozarta fararen hula a kasar, musamman ma mata da kananan yara. Ya ce, batun cin zarafin mutane a Sudan ta Kudu shi kadai ya isa ya tada hankalin al'ummar duniya.(Saminu)