Jakadan kasar Sin dake kasar Kenya Liu Xianfa da uwargidan shugaban kasar Kenya Margaret Kenyatta sun halarci bikin.
Har ila yau, bikin da ofishin jakadancin kasar Sin dake Kenya ya shirya, ya samun halartar kamfanonin Sin da dama, ciki har da kamfanin Weigao. Kuma an shirya samar wa Asusun "Beyond Zero" da ofishin uwargidan shugaban kasar Kenya ya kafa, wasu gadajen tiyata da akwatunan kiyaye zafin jikin jarirai da dai sauran na'urorin aikin jinya, wadanda gaba daya kudinsu ya kai dallar Amurka dubu 130, domin taimaka wa kasar Kenya kan ayyukan kiwon lafiya, musamman ma a fannin kiwon lafiyar mata da yara. (Maryam)