in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya za ta hada gwiwa da Sin wajen sarrafa shara
2017-12-03 13:02:32 cri

Kasar Kenya za ta kulla wata yarjejeniya da kasar Sin a watan Janairun shekarar 2018, domin inganta shirinta na sarrafa shara.

Geoffrey Wahungu, darakta janar na hukumar kare muhalli ta kasar Kenya (NEMA), ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi cewa, tuni aka tura tawagar wasu kwararru daga ma'aikatar kare muhallin kasar zuwa kasar Sin domin tattaunawa da takwarorinsu na kasar Sin kan nazarin yadda za'a aiwatar da yarjejeniyar.

Wahungu ya bayyana a lokacin taron kolin MDD kan batun tsarin kimiyya da cinikayya a fannin muhalli cewa, manufar kulla yarjejeniyar ita ce domin neman taimakon kasar Sin da ta samarwa kasar Kenyan kwararru da kuma fasahar zamani da ta fi karbuwa a duniya a fannin sarrafa shara.

Ya ce kasar Kenya ta shirya yin gwajin sarrafa shara na zamani a wasu yankunan kasar uku wadanda suka samu cigaba ta fuskar aiwatar da shirin sarrafa sharar.

Wahungu ya ce, idan shirin ya samu nasara, za'a aiwatar da shi a dukkan yankunan kasar baki daya domin hakan zai taimakawa kasar ta ci gajiyar samar da dauwamamman cigaban muhalli ta hanyar sarrafa shara.

A cewarsa, kasar Kenya tana neman sinawa masu zuba jari domin kafa wata masana'anta dake samar da makamashi ta hanyar shara.

Ya ce ya lura cewa, kasar Sin ta samu cigaba matuka wajen sarrafa dattin da masana'antu ke fitarwa don samun cigaba.

Ya kara da cewa, kasar Kenya za ta hada kai da kwararrun kasar Sin domin magance matsalolin shara da suka addabe ta.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China