A jiya ne kashi na uku na haramcin shiga kasar Amurka da gwamnatin Trump ta kakabawa wasu 'yan kasashe 8 ya fara aiki, bayan da ya samu amincewar kotun kolin kasar.
Hukuncin dai ya kawar da takunkumin da wasu kananan kotunan kasar suka saka, wanda ya haramtawa 'yan asalin kasashen Syria, da Iran da Chadi, da Yemen. Sauran sun hada da Somaliya da Libya da Koriya ta arewa da kuma wasu jami'ai daga kasashen Venezuela daga shiga kasar ta Amurka.
Sai dai a lokacin da take yanke hukunci, kotun kolin kasar Amurkar, ta ce bisa ga shawarar da wadancan kananan kotuna suka yanke, tana fatan kotun daukaka kara ta kasar, za ta bayar da nata shawarar da ta dace kan wannan al'amari.
A watan Satumban wannan shekarar ce dai aka sanar da wannan haramci, wanda ya kasance na uku da gwamnatin Trump din ta fitar. Gwamnatin dai tana cewa, ta dauki wannan mataki ne domin tabbatar da tsaron kasa, yayin a hannu guda kuma wasu biranen kasar ke cewa, wannan matakin nuna bambancin addini ne, duba da cewa, galibin kasashen da haramcin ya shafa, kasashen musulmi ne.(Ibrahim)