Shugaba Buhari, a yayin da yake karbar wasikun nuna jinjina daga wasu jami'an diplomasiyya a Abuja, yace, tun lokacin da aka kaddamar da sabon salon yakin da mayakan, kungiyar 'yan ta'addan ta fara fuskantar matsin lamba na rashin samun damar daukar karin sabbin mayakanta aiki.
Shugaban na Najeriya yace, kungiyar 'yan ta'addan ta rasa karfin ikon da take dashi a lokutan baya, inda a da ta kwace iko da wasu yankunan kasar, hakan ne ma ya sanya kungiyar ta buge da kaddamar da hare haren kunar bakin wake a tsakanin alummomin kasar, amma sannu a hankali za'a ga bayan kungiyar.(Ahmad Fagam)