Harin dai ya faru ne a yankin Kolofata dake arewacin kasar mai iyaka da Najeriya. Ana zaton mayakan sun kai harin ne a kokarin da suke na kwace kayan abinci daga mazauna wurin, yayin da kayan abincinsu ke shirin karewa.
Wani basarake a yankin Kolofata wanda ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce ya kamata jama'a su kasance cikin shirin aukuwar hare-haren mayakan daga lokaci zuwa lokaci, ganin yadda tun watanni da suka gabata mayakan na Boko Haram ke fama da karancin abinci.
Har ila a daren ranar Laraban, mayakan na Boko Haram sun mamaye wasu kauyuka dake kusa da yankin Mayo Moskota, inda suka tilastawa kauyawan arcewa garin Nguetchewa, da aka tura dakarun gwamnatin Kamaru.