Kakakin gwamnatin kasar Koriya ta Kudu Kim Eui-kyeom ya bayyana a yayin taron manema labarai cewa, ya zuwa yanzu, Kim Yong Nam ya kasance babban jami'i na farko cikin dukkanin jami'an Koriya ta Arewa da suka taba ziyartar kasar Koriya ta Kudu.
Hakan dai ya nuna aniyar kasar Koriya ta Arewa wajen kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma kyakyyawan fatan kasar na cimma nasarar gudanar da gasar.
Haka kuma, ya ce, a matsayin kasar da ta shirya gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na wannan karo, kasarsa za ta karbi tawagar wakilan kasar Koriya ta Arewa da hannu biyu-biyu, a sa'i daya kuma, kasar Koriya ta Kudu za ta yi shiri sosai, game da ganawa, da tattaunawar da za a yi a tsakanin jami'an kasashen biyu. (Maryam)