A daren ranar 9 ga wata ne, Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu suka fidda wata sanarwar hadin gwiwa, bayan ganawar wakilan kasashen biyu a Panmunjom, inda suka bayyana cewa, bangarorin biyu sun cimma matsaya kan ziyarar tawagar masu fasaha ta kasar Koriya ta Arewa za ta kai kasar Koriya da Kudu da yin shawarwarin a tsakanin hukumomin sojoji na kasashen biyu da sauran batutuwa
Haka kuma, sun jaddada cewa, bangarorin biyu za su tattauna a fannoni daban daban, domin warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari. (Maryam)