Wakilin musamman na babban sakataren MDD da ke Sudan ta kudu Ellen Margrethe Loj ya sake nanata kudurin MDD na kare rayukan fararen hula da ke kasar.
Kakakin MDD Stephane Dujarric wanda ya bayyana hakan yayin ya ke yiwa manema labarai karin bayani, ya kuma bayyana cewa, Ellen Loj ya bukaci dukkan bangarorin kasar da su guji daukar duk wasu matakai ko furta kalaman da ka iya rura wutar rikici. Kana su martaba dokokin da suka shafi wuraren da MDD ta kebe don tsugunar da fararen hula, ciki har da dokar nan da ta haramta shiga da makamai cikin wadannan wurare.
Manzon na MDD ya yi wadannan kalaman ne a jiya Talata lokacin da ya ziyarci garin Malakal da ke yankin arewa maso gabashin Sudan ta kudun domin ganewa idonsa halin da ake ciki, sannan ya gana da bangarorin da ke wurin, ciki har da shugabannin al'umma da ke wuraren kare fararen hula da aka tanada da ke garin na Malakal.
A ranar 18 ga watan Fabrairu ne wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne suka kai hari kan sansanin MDD da ke garin Malakal, fadar mulkin jihar Upper Nile da ke Sudan ta kudun, inda suka halaka mutane a kalla 7, kana wasu da dama kuma suka jikkata.(Ibrahim)