A shekarar 2009 ne, Angola da Rasha suka cimma yarjejeniyar hadin gwiwa kan harba wannan tauraron dan Adam, kuma an fara gudanar da aikin a shekarar 2012, matakin zai kyautata hidimar sadarwa da watsa labaru ta telebijin da rediyo a kasar Angola tare da rage kudin da ake kashewa a wannan fanni. (Zainab)