Da yake ganawa da manema labarai a wani bangare na taron karawa juna sani dake da nufin karfafa tsarin kiwon lafiyar al'umma a kasar, Michel Kouakou ya ce ayyukan shirin za su ci gaba da mayar da hankali wajen taimakawa Gwamnati daukar matakan yaki da cutar.
Ya ce shirin UNAIDS ya kasance ya na taimakawa Gwamnati aiwatar da shirin da aka yi wa lakabi da 'gwaji da magani' da aka kaddamar a watan Yunin da ya gabata domin dukkan masu dauke da cutar.
Ya ce manufar ita ce, daga nan zuwa 2030, shirin ya kai ga kaso 90 cikin dari na mutanen da ke dauke da cutar kanjamau wadanda ke karbar magani. (Fa'iza Mustapha)