Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Amurka, ta jaddada matsayin kasar game da shirin ta, na ficewa daga yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi, da zarar ta kammala shirye shiryen hakan.
Amurka dai ta sha alwashin yin sallama da 'yarjejeniyar, muddin dai ba a sauya wasu sassa na yarjejeniyar ba, wadanda a cewar mahukuntan kasar na da cutarwa ga Amurkawa.
Amurka ta shiga yarjejeniyar Paris ne a shekarar 2015, karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Barack Obama, yarjejeniyar da ta yi kira ga kasashen duniya kimanin 200, da su amince da matakan rage fitar da iska mai gurbata muhalli.
Duk dai da matakin da Amurkar ke niyar dauka, sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta fitar a baya bayan nan, ta ce kawo yanzu ba a riga an kammala daukar matakin ba.(Saminu)