Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang wanda ya bayyana hakan Larabar nan yayin taron manema labarai da aka saba yi a nan birnin Bejing, ya ce kasar Sin ta bukaci Koriya ta arewa da ta martaba kudurorin kwamitin sulhu na MDD, kana ta yi watsi da duk wani mataki da zai kara tsananta halin da ake ciki a zirin koriya.
A yau da safe ne gidan Talabijin na Koriya ta arewan ya ba da rahoton cewa, kasar ta yi nasarar gwada harba wani makami mai linzami da ta kera wanda ka iya kaiwa wata nahiya.(Ibrahim)