in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Qatar ta bayyana aniyar gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa na 2022 ba tare da gurbata muhalli ba
2017-11-29 09:49:54 cri
Kasar Qatar ta ce ta shirya karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na hukumar FIFA a shekarar 2022, ta hanyar amfani da na'urorin da ba sa fitar da hayaki mai gurbata muhalli.

Kamfanin dillancin labarai na kasar ta Qatar QNA, ya rawaito wani kusa a kasar ta Qatar Essa bin Hilal al Kuwari, na bayyana hakan yayin da yake gabatar da jawabi, a madadin ministan ma'aikatar makamashi da masana'antu na kasar Mohammed bin Saleh al Sada, a bikin bude taron "wanzar da ci gaba" wanda ya gudana a Doha a ranar Lahadi.

Al-Kuwari ya ce "Qatar na fatan gudanar da gasa da ba za ta haifar da fitar da hayakin carbon mai gurbata muhalli ba. Don haka dukkanin na'urori da za a yi amfani da su a yayin gasar, za su zamo masu tsarin (GSAS) wadanda hukumar ta FIFA ta amince da su".

Ya ce Qatar din ta tsara wani shiri da za a aiwatar nan da shekaru 5 masu zuwa, wanda zai bada damar yin tsumin ruwa da kaso 35 bisa dari, da kuma tsumin lantarki da 25 bisa dari.

Kaza lika kasar na fatan rage jimillar hayakin carbon mai gurbata iska da ake fitarwa a cikin kasar nan da shekarar 2022 da kimanin tan miliyan 6.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China