in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An jinkirta zaben sabbin mambobin nahiyar Asiya a majalisar hukumar FIFA
2016-09-28 19:48:28 cri
A baya an tsara cewa, za a gudanar da zaben sabbin mambobin nahiyar Asiya na majalisar hukumar FIFA, wanda za a yi a kasar Indiya a ranar 27 ga wata, sai dai sakamakon rashin cimma daidaito game da ajandar taron, an dage lokacin wannan zabe.

Game da shirya wannan zabe, hukumar wasan kwallon kafa ta nahiyar Asiya, ta gudanar da taron musamman na wakilan hukumar. An jefa kuri'u game da ajendar taron, kuma yawancin membobi mahalartar taron sun jefa kuri'un kin amincewa. A karshe, an samu kuri'un kin amincewa 42, da kuri'ar nuna amincewa 1, don haka aka soke sauran ayyukan da za a gudanar a gun taron. Daga baya, shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta Asiya Yarima Salman ya sanar da rufe wannan taro.

A yayin taron gaggawa na kwamitin hukumar wasan kwallon kafa ta Asiya da aka gudanar a baya, Yarima Salman ya bayyana cewa, an samu hadin kai a tsakanin mambobin hukumar wasan kwallon kafar Asiya, da dandalin wasan kwallon kafa na Asiya, kana ya nuna godiya ga membobin hukumar bisa nunawa kasa da kasa ra'ayi na bai daya da suke bi.

A daya hannun kuma, an nada mataimakin shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Sin Zhang Jian, a matsayin memban kwamitin hukumar wasan kwallon kafar ta Asiya, kuma wa'adin aikin sa ya fara ne daga yanzu zuwa lokacin da ake gudanar da taron mambobin hukumar na nan gaba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China