in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump: Amurka za ta fice daga yarjejeniyar Faris ta sauyin yanayi
2017-06-02 09:09:21 cri

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce ya yanke shawarar fitar da kasar sa daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Faris, yarjejeniyar da ta zamo jigo ga yunkurin da kasashen duniya ke yi na dakile tasirin sauyin yanayi.

Shugaba Trump wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a fadar White House, ya ce gwamnatin sa za ta dakatar da duk wasu hidimomi na kudi masu alaka da wannan yarjejeniyar, wadda ya ce tana cike da rashin adalci.

Sai dai ya ce, nan gaba Amurkar za ta nemi sake shiga yarjejeniyar bisa sharadin yi mata adalci a fannin rawar da za ta taka tsakanin sauran kasashen duniya da suka amince da yarjejeniyar. Ko da yake ya ce, sake yiwa yarjejeniyar kome ba wani muhimmin kuduri ne ga gwamnatin sa ba.

Trump dai ya yanke shawarar fitar da Amurka daga wannan yarjejeniya ne a wani mataki na cika alkawarin da ya yiwa Amurkawa, yayin da yake yakin neman zaben sa, ko da yake ga alama matakin zai hadu da tirjiya daga gida da kuma kasashen waje.

Tuni gwamnan jihar California Jerry Brown, ya sha alwashin kalubalantar wannan mataki na ficewar Amurka daga yarjejeniyar ta Faris.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China