in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na shirin zama babbar cibiyar raya yawon shakatawa ta jiragen ruwa
2016-11-14 10:07:28 cri

Mahukuntan kasar Sin na daukar matakan raya fannin yawon shakatawa ta jiragen ruwa, a wani mataki na mayar da kasar wata cibiya mafi girma a wannan fanni tsakanin kasashen dake yankin Asiya da Fasifik. Wannan mataki dai na zuwa ne a gabar da harkar yawon bude ido ta ruwa, ke dada samun tagomashi tsakanin al'ummar Sinawa a cikin gida.

A cewar mataimakin shugaban hukumar raya yawon shakatawa ta kasar Sin Li Shihong, alkaluman da tashoshin jiragen ruwan yawon bude ido dake kasar suka fitar, sun nuna cewa, irin wadannan jirage 629 ne suka yi dakon masu yawon bude ido a shekarar 2015.

Mr. Li wanda ya bayyana hakan yayin wani taro na tattauna batutuwan yawon shakatawa, tsakanin babban yankin kasar Sin da yankunan Hong Kong da Macao, ya ce yanzu haka manyan kamfanonin jiragen ruwa na 'yan yawon bude ido guda 5, sun riga sun shiga kasuwannin kasar Sin, wanda hakan ya daga matsayin kasar ta Sin a fannin.

Kaza lika jami'in ya bayyana aniyar kasar Sin game da bunkasa wannan fanni, inda tuni aka fara shawarar gina tashoshin jiragen ruwa na 'yan yawon shakatawa a lardin Guangdong, da yankin Hong Kong da kuma Macao, wadanda za su zamo muhimman tashoshi na jiragen ruwan.

A ranar Asabar ne dai aka bude tashar jiragen ruwa ta 'yan yawon bude ido mafi girma a kasar Sin a birnin Shenzhen, tashar da za ta iya daukar jiragen ruwan da nauyin su ya kai tan 220,000.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China