Masu gabatar da kara na gwamnatin Amurka sun shigar da karar wanda ake zargi da kai harin birnin New York gaban kotu, inda suke tuhumarsa da laifin ta'addanci.
Mukaddashin Atoney Janar na lardin kudancin New York Joon Kim ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a jiya Laraba.
Wanda ake zargin Sayfullo Saipov, da a yanzu haka ke tsare, na fuskantar tuhume-tuhume 2 da suka hada da ba da taimako ga kungiyar IS da laifin tada zaune tsaye da rashin daraja rayuwar bil adama da gangan.
A cewar Joon Kim, idan aka yanke masa hukunci, zai iya fuskantar daurin rai da rai ko hukuncin kisa.
Yayin taron manema labaran, mataimakin kwamishinan 'yan sandan birnin John Miller, ya ce Sayfullo Saipov da ya kaura daga Uzbekistan, ya shafe makonni yana tsara yadda zai kai harin da aka kira mafi muni da aka kai birnin tun bayan na ranar 11 ga watan Satumban 2001.
A ranar Talata da ta gabata ne Saipov dake cikin motar a kori kura ya kutsa kan hanyar masu keke da tafiya da kafa a Manhattan, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 8 da raunata 12. Daga bisani, 'yan sanda sun harbe shi, inda kuma aka garzaya da shi asibiti. (Fa'iza Mustapha)