Ma'aikatar ta ce kudaden cinikayya cikin watanni 3 na farkon shekarar nan, sun kai kwatankwacin dalar Amurka biliyan 200, wanda hakan ke nuna karin kaso 32.1 bisa dari idan an kwatanta da bara, karuwar da kuma ta kusa ninka wadda aka samu a bara.
Ma'aikatar cinikayyar ta ce, harkokin da ke kan gaba wajen samun ci gaba sun hada da fannin yawon shakatawa, da na sayar da abinci, da na nishadantarwa, inda harkokin sayar da abinci na tafi da gidanka, suka samu karuwar cinikayya da kaso 64 bisa dari, yayin da na sayar da tikitin tafiye tafiye, suka karu da kaso 163 bisa dari sama da na bara.
Sinawa sun kara yawan sayayya a fannin tufafi, da tabarau masu amfani da na'urori, da kuma ababen hawa masu amfani da fasahohin zamani.
Kamfanonin cinikayya na yanar gizo kamar su Alibaba da JD.com, sun fadada hidimomin da suke baiwa abokan huldarsu, inda a yanzu suka kara yawan lokutan bada hidima, daidai da bukatun kasuwani na zamani. (Saminu Hassan)