in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta fice daga yarjeneiyar nukiliyar kasar Iran
2017-10-14 11:50:25 cri
A jiya ne shugaba Trump na kasar Amurka ya bayyana cewa, ya yanke shawarar ficewa daga yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran da aka cimma a shekara ta 2015.

Shugaba Trump ya bayyanawa taron manema labarai a fadar White House cewa, bisa ga wasu muhimman bayanai da aka gabatar masa, Amurka ba za ta ci gaba da kasancewa a cikin wannan yarjejeniya ba.

Bugu da kari, Trump ya yi barazanar cewa, a kowa ne lokaci zai iya soke wannan yarjejeniya da aka cimma a shekarar 2015 tsakanin Iran din da kasashe Burtaniya, Sin, Faransa, Rasha da Amurkar da kuma Jamus.

Kamar yadda dokar da ta shafi yarjejeniyar nukiliyar ta kasar Iran da aka yiwa gyaran fuska (INRA) wadda majalisar dokokin Amurka ta amince da ita a shekarar 2015. Gwamnatin Amurkar tana da kwanaki 90 ta sanar da majalisar dokokin kasar game da nuna kin amincewarta da wannan yarjejeniya. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China