Rahotanni daga Tarayyar Najeriya na cewa, murar tsuntsaye ta hallaka kaji da yawan su ya kai 42,000 a jihar Plateau dake tsakiyar kasar, tun bayan barkewar cutar a watan Janairun da ya gabata. Wannan annoba dai ta haifar da dunbin asara ga masu kiwon kaji a jihar, baya ga barazana da take yi ga lafiyar masu cin kajin.
Kungiyar masu kiwon kaji ta kasar reshen jihar Plateau ta bayyana cewa, cikin 'yan makwannin baya bayan nan an kashe dubban kaji a gonaki da dama sakamakon bullar wannan cuta, a wani mataki na dakile yaduwar ta.
Da yake karin haske game da lamarin, shugaban kungiyar masu kiwon kaji a jihar John Dasar, ya ce bisa jimilla, cutar ta shafi gidajen kaji da yawan su ya kai 12, a sassan jihar daban daban.(Saminu Alhassan)