in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Namibiya ta kaddamar da shirin kungiyoyin gama kai na shekarar 2017
2017-08-11 09:44:38 cri

Ministan ma'aikatar aikin gona, albarkatun ruwa da gandun daji na kasar Namibiya John Mutorwa, ya kaddamar da wani shirin kungiyoyin hada kai na shekarar 2017.

A lokacin kaddamarwar, Mutorwa, ya bayyana cewa a halin yanzu akwai kungiyoyin hada kai kimanin 146 a kasar ta Namibiya, kuma mafi yawan kungiyoyin a fannin aikin gona ne, da kuma wasu da dama daga bangaren hakar ma'adanai, da masana'antu, da harkokin kudi da sana'o'in hannu.

Mutorwa, ya kara da cewa, manufar tsarin kafa kungiyoyin ita ce, domin hada kan al'ummar kasar ta Namibiya wajen samar da ci-gaba, da kuma tabbatar da ba da 'yanci ga hukumomi masu zaman kansu.

Ministan ya nuna cewa, yana da kwarin gwiwa kan ganin tsarin kungiyoyin hada kan ya taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da tsare-tsare masu kyau ga manoma, da masu hakar ma'adanai, da masu aikin masana'antu, da 'yan kasuwa, ta yadda za su samu damar ajiya da kuma karbar basussuka a kungiyance don tsara dabarun da za su kara bunkasuwa, wanda hakan zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin kasar ta Namibiya.

Kungiyoyin hada kan za su kasance a matsayin wata gada ce ga al'ummar kasar ta Namibiya, musamman wajen tallafawa masu fama da talauci a tsakanin al'umma, ta yadda za su iya shiga a dama da su wajen ayyukan ciyar da tattalin arzikin kasar gaba, wanda hakan mataki ne da zai baiwa kasar Namibiya damar tsayawa da kafafunta ta fuskar ci-gaban tattalin arziki.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China