An mika tallafin ne a hukumance tsakanin mataimakin ministan harkokin wajen Sin Zhang Ming da ya kai ziyara kasar, da mataimakiyar firayiministan Namibia kuma ministar harkokin wajen kasar, Netumbo Nandi-Ndaitwah.
Netumbo Nandi-Ndaitwah ta ce fari a Namibia ya shafi mutane sama da 595,000, inda shugaban kasar Hage Geingob ya ayyana shi a matsayin matsalar dake bukatar daukin gaggawa.
Ministar ta kara da cewa, wannan gagarumar gudunmawa ce, inda tuni aka aike da adadi mai yawa zuwa yankuna da wadanda aka bayar dominsu. (Fa'iza Mustapha)