Staffan de Mistura wanda ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da manema labarai jiya da daddare, ya ce an kammala zagaye na 7 na tattaunawar, inda ya ce an dan samu karin ci gaba, domin babu wanda ya fice haka zalika babu matsala da aka samu.
Ya ce ya na jin cewa, mutanen da ya tattauna da su a wannan makon, na goyon bayan abun da suke son cimmawa.
De Minstura ya kuma sanar da cewa, za a fara sabon zageyen tattaunawar a farko watan Satumba.
Da yake bada amsa kan tambayar da aka masa game wata tawaga da Faransa ta kafa, de Mistura ya ce ya tuntubi ayarin sosai, wanda Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya samar kwanannan, kan yadda kasarsa za ta bada gudunmuwa ga aikin da MDD ta ke kan batun Syria.
Faransa ta kira jerin taruka da Rasha da kuma Amurka ciki har da Shugaba Donald Trump, inda shugaban na Amurka ya yi maraba da wannan yunkuri da zai taimakawa tattaunawar zaman lafiya a Syria, wanda alama ce dake nuna cewa Faransa za ta fara taka muhimmiyar rawa a tattaunawar. (Fa'iza Mustapha)