A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, ya bayyana cewa kasashen biyu sun cimma matsaya game da kawo karshen kaddamar da hare hare a wadannan yankuna. Ya kuma ce yarjejeniyar da aka cimma idan har ta yi nasara, na iya zama ginshikin kawo karshen dauki ba dadi a wasu karin sassan kasar ta Syria.
Wannan shiri dai na tsagaita bude wuta, bangare ne na fadada matakai da aka amince za a dauka tun cikin watan Mayun da ya gabata a sassan kasar ta Syria hudu, ciki hadda yankunan kudancin kasar inda fada ke kara kazanta, matakin da ya sanya Amurka da Rasha cimma wannan yarjejeniya ta tsagaita bude wuta. (Saminu)