Mahukuntan yankin Singida a tsakiyar kasar Tanzaniya sun dakatar da kamun kifi har na tsawon shekara guda a tafkin Kitangiri saboda ceto kananan koramun kasar daga bacewa.
Kitangiri, daya ne daga cikin koramun kasar na soda lakes, wanda ya hade yankunan kasar biyar da suka hada da Iramba, Igunga, Meatu da Kishapu, kuma wannan haramci ya shafi dukkan yankunan baki daya
Emmanuel Luhahula, shi ne kwamishina mai kula da gundumar Iramba , ya fada cewa, za'a rufe kamun kifin ne daga ranar 1 ga watan Yuli na wannan shekara zuwa 30 ga watan Yunin shekarar 2018.
Ya zayyana batutuwa da suka hada da tsananin kamun kifi, da yin kamun kifin ba bisa ka'ida ba, da gurbata muhalli, a matsayin dalilan dake haifar da barazana ga kananan koramun kasar.
Luhahula ya kara da cewa, yawan karuwar jama'a da sauyin yanayi suma dalilai ne da suka sa aka rage yawan dogaro kan noma da kiwon dabbobi inda aka raja'a kan kamun kifi.
A cewarsa wadannan su ne dalilan da suka sa aka dakatar da dukkan wasu ayyukan da suke da nasaba da bil adama wanda ke illata albarkatun, kuma daukar wannan matakin zai iya ceto wadannan albarkatun da Allah ya huwace su a kasar.
Jami'in ya ce, kamun kifi ta haramtattun hanyoyi shi ne hanyar ta farko mafi zama barazana ga dorewar wadannan koramu, wannan shi ne dalilin da ya sa suka yanke shawarar haramta kamun kifin baki daya. Wannan haramci a cewarsa zai inganta rayuwar kifayen dake wadannan koramu.(Ahmad Fagam)