A jiya ne shugaba John Magufuli na kasar Tanzaniya ya kaddamar da kamfanin mulmula karafa mai jarin kasar Sin na Kiluwa dake gabashin gundumar Kibaha ta kasar Tanzaniya.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da kamfanin, shugaba Mugufuli ya yaba da yadda masu zuba jari na kasar Sin suka zabi kasar Tanzaniya domin su zabu jarin su, inda ya yi kira ga sauran masu zuba jari na ketare da su yi koyi da Sinawan.
Shugaba Magufuli ya ce, wannan wani muhimmin mataki ne a kokarin da gwamnatinsa ke yi na raya bangaren masana'antun kasar, duba da yadda kasar ta Tanzaniya ke samar da bakin karfe mai inganci wanda ya dace da matsayin kasa da kasa, da a halin yanzu ake amfani da shi wajen gina gadoji a sassa daban-daban na duniya.
Ya kuma ja hankalin 'yan kasar da su guji shigo da albarkatun da kamfanonin ke bukata, ganin yadda Allah ya horewa kasar tarin tama ko bakin karfe a yankin Mchuchuma dake kudancin kasar.
Kashin farko na kamfanin mulmula karafa na Kiluwa zai iya samar da tan 300,000 na bakin karfe a shekara. Yayin da kashi na biyu na kamfanin zai iya samar da a kalla tan 1,200,000 na bakin karfe a shekara.(Ibrahim)