A yayin taron manema labarai da aka yi a wannan rana, Xie Xiaoyan ya ce, kasar Sin tana sa ran za a kulla wasu yarjejeniyoyi a yayin taron shawarwarin neman sulhu, da aiwatar da su yadda ya kamata, ta yadda za a samu fahimta a tsakanin kabilu daban daban na kasar Syria, sa'an nan, za a iya samun fahimtar juna a tsakanin kabilu da gwamnatin kasar ta Syria.
A sa'i guda kuma, kasar Sin ta dukufa wajen ba da taimakon jin kai ga al'ummomin kasar, ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar Sin ta samar da taimakon jin kai da darajar su ta kai dallar Amurka miliyan 680 ga kasar Syria da wasu kasashen dake yankin.
Bugu da kari, Mr. Xie ya jaddada cewa, 'yan ta'adda su ne abokan gaba na dukkanin bil Adama a nan duniya, ya kamata bangarori daban daban na kasar Syria, da kasashen dake yankin da kuma gamayyar kasa da kasa su yi hadin gwiwa wajen yaki da ta'addanci, bai kamata a nuna bambanci a yayin gudanar da ayyukan yaki da ta'addanci ba. (Maryam)