Hukumar bunkasa ilmi, kimiyya da raya al'adu ta MDD UNESCO ta nuna damuwa game karuwar rashin ilmi a kasashen dake yankin kudu da hamadar Saharar Afrika.
Wani kwararre a fannin kimiyya a ofishin dake kula da kasashen gabashin Afrika na hukumar, Abdul Lamin ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi cewa, bisa ga alkaluma, ana samun raguwar kashi biyu bisa dari na yawan masu ilmi a kasashen hamadar Saharar Afrika a duk shekara.
Lamin ya ce, ana samun karuwar yawan marasa ilmin ne sakamakon wasu kalubaloli da suka hada da karuwar yawan jama'a da karancin zuba jari a fannin makarantun gwamnati, ya fadi hakan ne a lokacin wani taron shiyya da UNESCO ta shirya da nufin nazartar hanyoyin bunkasa ci gaban ilmi da kuma cimma nasarar shirin raya ilmi na muradin karni karkashin shirin ajandar dawwamamman ci gaban ilmi a kasashen hamadar Saharar Afrika nan da shekarar 2063.
A cewar hukumar ta MDD, akwai mutane kimanin miliyan 203 da suka haura shekaru 15 wadanda ba su da ilmi a kasashen yankin.
Kaso mafi yawa na mutanen sun kunshi 'yan kasashen Demokaradiyyar Kongo, Nijeriya, Habasha, Kenya, Uganda, da Tanzania.(Ahmad Fagam)