A yau talata shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon ta'aziyya ga sarauniyar Ingila Elizabeth II sakamakon fashewar abubuwa a birnin Manchester na kasar Birtaniya.
A sakon da ya aika, shugaba Xi ya nuna juyayi ga mutanen da lamarin ya rutsa da su, kana ya mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon fashewar.(Ahmad Fagam)