Yanzu haka dai ana gudanar da taron yini biyu tsakanin Larabar nan zuwa gobe Alhamis, musamman domin zakulo hanyar warware rikicin Syria, taron dake gudana a birnin Astana, fadar mulkin kasar Khazakstan.
Rahotanni dai na nuna cewa mahalarta taron na da sabanin ra'ayi game da wasu batutuwa masu yawa.
Game da hakan ne kuma, Mr. Gang Shuang ya ce, makasudin taron shi ne kokarin tabbatar da kudurin tsagaita bude wuta a Syria, kuma kasar Sin na fatan ganin bangarorin masu ruwa da tsaki za su yi amfani da wannan dama, domin kara musayar ra'ayi, da nuna sahihanci, gami da tabbatar da amincewa juna, ta yadda za a share fagen shawarwarin da za a gudanar nan gaba, da samar da gudunmowa ga yunkurin daidaita rikicin kasar ta Syria a siyasance. (Bello Wang)